Freedom Radio Nigeria Kiwon Lafiya Shugaba Buhari ya kaddamar da sabbin jiragen shalkwabta guda 2

Shugaba Buhari ya kaddamar da sabbin jiragen shalkwabta guda 2Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce yaki da ‘yan ta’adda da dakarun kasar nan ke yi a wannan lokaci, yana haifar da ‘Da’ mai ido.

Shugaba Buhari ya ce sojoji ba ko shakka cikin shekara hudu da suka gabata, sojojin kasar nan suna aiki tukuru domin dakile matsalolin tsaro a Najeriya.

Shugaban kasar wanda mataimakin sa farfesa Yemi Osinbajo ya wakilta ya bayyana hakan ne a dandalin Eagles Square da ke Abuja, yayin wani bikin cika shekaru hamsin da biyar da kafa rundunar sojojin sama na kasar nan.

A yayin taron shugaban kasar ya kuma kaddamar da wasu sabbin jiragen shalkwabta guda biyu da rundunar sojin saman kasar nan ta saya abaya-bayan nan.

Da ya ke gabatar da nashi jawabi, babban hafsan sojin sama na kasar nan Air Marshal Sadique Abubakar, ya ce, rundunar za ta ci gaba da kokari don dakile ayyukan batagari.