Freedom Radio Nigeria Kiwon Lafiya Najeriya kasa ta uku da ta fi kowacce kasa yawan mutane masu mutuwa a shekaru 50

Najeriya kasa ta uku da ta fi kowacce kasa yawan mutane masu mutuwa a shekaru 50Hukumar kidaya ta majalisar dinkin duniya ta bayyana Najeriya a matsayin kasa ta uku a duniya da mafi yawa na al’ummar kasar basa haura shekaru hamsin da biyar a duniya suke mutuwa.

Rahoton hukumar wanda aka wallafa jiya Litinin ya bayyana cewa an samu dama-dama a shekarar 2019 na adadin al’ummar Najeriya da suke mutuwa ba tare da sun haura shekaru hamsin da biyar ba, idan akwa kwatanta da kasasken Sierra Leone da Chadi da kuma Jamhuriyar Afirka ta tsakiya.

A cewar rahoton hukumar a kasashen Sierra Leone da Chadi da kuma Jamhuriyar Afirka ta tsakiya al’ummomin basa haura shekaru hamsin da uku zuwa da hudu suke mutuwa.

Sai dai rahoton ya kuma bayyana cewa kasashe irin su Afghanistan Somaliya da kuma Syria al’ummomin kan haura shekaru hamsin da tara zuwa sittin da biyar ko kuma saba’in da uku.

 

Kamar yadda rahotanni ya bayyana Najeriya na da kaso arba’in da hudu cikin dari na matsalar auren wuri da ake yiwa kananan yara, yayinda ake da kaso goma sha biyar zuwa sha tara na auren wadanda shekarun su suka kai mizanin da ake so.