Freedom Radio Nigeria Manyan Labarai Majalisar dokokin jihar Kano ta yadda da kara sarakunan yanka guda hudu

Majalisar dokokin jihar Kano ta yadda da kara sarakunan yanka guda huduMajalisar dokokin jihar Kano ta sahale ga gyaran dokar masarautu ta jihar Kano wadda ta amince da kafa sabbin Sarakunan yanka masu daraja ta daya a jihar ta Kano guda hudu.

Hakan ya biyo bayan amincewa da sakamakon rahoton da shugaban masu rinjaye na majalisar Baffa Babba Dan-Agundi ya karanta.

Bayan daukar tsawon lokaci ‘ya’yan majalisar na zaman sirri kan batun dawowar su ke da wuya suka amince da dokar.

Da ya ke Karin haske kan dokar shugaban masu rinjaye na majalisar Baffa Babba Dan-Agundi, ya ce, jikokin Sarki Dabo su za su ci gaba da sarautar masarautar Bichi haka zalika masu nadin sarautar Kano su zasu zabi Sarki a kasar Bichi.

Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Danbatta ya kalubalanci lamarin yana mai cewa ba a yi adalci wa arewacin Kano ba sakamakon cewa sarakuna uku daga cikin hudu sun fitone daga kudancin Kano.

Yayin da a bangare guda majalisar ta amincewa gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da ya nada mai shari’a Nura a matsayin babban jojin jihar Kano.