Freedom Radio Nigeria Labarai,Manyan Labarai JAMB ta saki sakamakon jarabawar UTME na bana

JAMB ta saki sakamakon jarabawar UTME na banaHukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantun gaba da sakandire ta kasa JAMB ta saki sakamakon jarabawar UTME da dalibai suka rubuta a watan jiya na Afrilu.

Shugaban hukumar ta JAMB farfesa Ishaq Oloyede ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai yau Asabar a Abuja.

Farfesa Ishaq Oloyede ya kuma nemi afuwan al’ummar kasar nan sakamakon tsaikon da aka samu wajen fitar da sakamakon jarabwar.

Ya ce, an saki sakamakon dalibai miliyan daya da dubu dari bakwai da casa’in da biyu da dari bakwai da goma sha tara, yayin da kuma aka rike sakamakon wasu dalibai dubu talatin da hudu da dari daya da ashirin ciki kuwa har da wasu dubu goma sha biyar da dari daya da arba’in da biyar wadanda aka gano cewa tagwaye ne.

Ya kuma bukaci dalibai da su yi amfani da lambobin wayoyin su da suka yi rajista wajen aikawa da sako ta kan wannan lamba 55019, domin duba sakamakon su.