Freedom Radio Nigeria Labarai Cibiyar CITAD ta ja kunnen fasinjoji kan kula da kayan su a filayen jirage

Cibiyar CITAD ta ja kunnen fasinjoji kan kula da kayan su a filayen jirageCibiyar bunkasa fasahar sadarwa da ci gaban al’umma, CITAD ta yi kira ga fasinjojin jirgin sama da su rinka isa filin jirgin sama kan lokaci don samun damar auna kayansu cikin lokaci tare da sanya ido sosai kayan kayan nasa don gujewa sanya musu kayan matsala.

Jami’in gudanarwar na cibiyar, Malam Isah Garba ne ya bayyana haka yau a wajen taron manema labarai da cibiyar ta gudanar a nan Kano.

Malam Isah Garba ya ce la’akari da yadda aka zargi wasu jami’ai a filin jirgin saman Malam Aminu Kano da sanya kwaya a kayan wata fasinja, akwai bukatar matafiya su rinka kula sosai.

Cibiyar ta kuma bukaci hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA da ta ci gaban da sanya ido soasai da nufin tabbatar da ba a sake sanya wa wani kwaya a kayan wani.

Cibiyar ta kuma jaddada bukatar a hukunta duk wanda aka kama da laifin cusa kwaya a kayan matafiya a filin jirgin Malam Aminu Kano kasancewar kotu ta bada belin su.