Freedom Radio Nigeria Kiwon Lafiya Fitacciyar ‘yar jarida Zainab Umar Ubale ta rasu

Fitacciyar ‘yar jarida Zainab Umar Ubale ta rasuFitacciyar ‘yar jaridar nan da ke gidan rediyon Rahama a nan Kano, Hajiya Zainab Umar Ubale ta rasu a da safiyar yau Laraba 22 ga watan Mayu 2019.

Marigayiya Zainab Umar Ubale ta rasu ne a dalilin haihuwa.

An kuma gudanar da jana’izar ta a unguwar Shagari Quaters da ke nan birnin Kano da misalin karfe 3:00 na yamma inda al’umma da dama suka halarci jana’izarta.

Ta kuma rasu ne ta bar mai gidanta da ‘ya’ya hudu.