0 Comments

Gwammatin tarayya ta yi Karin girma ga jami’an tsaro na Civil Defence, da jami’an hukumar kashe gobara, da ma’aiktan hukumar kula da gidajenn yari da kuma jami’an hukumar kula da shige da fice su18,954  guda Dubu goma sha takwas da dari tara da hamsin da hudu.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren majalisar koli dake kula da hukumomin 4 Al-hassan Yakmut.

Sanarwar ta ce, kimanin manyan jami’an hukumar kula da shige da fice ta kasa 884 ne suka sami karin girma, yayin da kuma na hukumar kula da gidajen yari ta kasa 6,179 suka samu karin girman.

Sauran wadanda aka yiwa karin girmar sun hada da: jami’an hukumar tsaron Civil Defence  3,488 suka samu karin girma, sai kuma jami’an hukumar kashe gobara 440 da aka yiwa karin girman.

Share
Share
Language »