Freedom Radio Nigeria Labarai Kungiyar ASUP ta janye yajin aikin da ta shirya farawa

Kungiyar ASUP ta janye yajin aikin da ta shirya farawaKungiyar malaman kwalejojin kimiyya da fasaha ta kasa ASUP reshen kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Kano, ta janye shirin fara yajin aikin mako guda da ta shirya za ta fara a jiya Alhamis.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar Dr. Ahmad Zubair Chedi.

Sanarwar ta ce kungiyar ta ASUP, ta yanke shawarar janye yajin aikin da ta so farawa a jiya ne sakamakon taron gaggawa da ta gudanar a jiyan.

A cewar sanarwar, mambobin kungiyar sun gamsu da shiga tsakani da ma’aikatar kula da manyan makarantu ta jihar Kano ta yi da sanya bakin masu ruwa da tsaki da kuma nuna damuwa da ita kanta gwamnatin jihar Kano ta yi kan lamarin.