Freedom Radio Nigeria Labarai Shugaba Bahari ya soki Shugabannin dokokin tarayya

Shugaba Bahari ya soki Shugabannin dokokin tarayyaShugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana Shugabannin majalisun dokokin tarayya Sanata Bukola Saraki da Yakubu Dogara a matsayin wadanda ke da karancin kishin kasa.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne lokacin da ya ke hira ta musamman da gidan talabijin na NTA a daren jiya.

A cewar shugaba Buhari ko kadan bai ji dadin halayyar Shugabannin majalisun biyu ba sakamakon yadda suka rike kasafin kudin bana a wajen su har na tsawon watanni bakwai saboda kawai bukatun kashin kansu.

Haka zalika shugaban kasar ya kuma ce rundunar ‘yan sandan Najeriya da Shugabannin al’umma sun gaza matuka wajen gudanar da hakkokin da ya rataya a wutar su.

Sai dai ya ce yana fata ‘yan sanda da bangaren shari’a za su kara zage dantse wajen aiwatar da hakkokin da ya rataya a wuyar su a zangon mulkin sa na biyu.