0 Comments

Babban sefeton ‘yan sanda na Najeriya Muhammadu Adamu ya bada umarnin da a gaggauta mayar da kwamishinan ‘yan sanda Ahmad Iliyasu zuwa jihar Kano a matsayin sabon kwamishina  bayan da wa’adin aiki na CP Wakili Mohammed ya kare.

A ranar 26 ga watan da muke ciki ne wa’adi aikin kwaminan ‘yan sanda Wakili Mohammed ya kare bayan ya kai shekaru 35 yana aiki.

Sabon kwamishinan ‘yan sandan na jihar Kano Ahmed Iliyasu na rike da digiri na 2 kan harkokin kasuwanci daga jam I’ar Ambrose Ali da ke Ekpoma kafin daga bisani a mayar da shi shalkwata rundunar ‘yan sanda dake Abuja, a matsayin babban jami’I.

Haka kuma a shekara ta 2016 zuwa watan Junairun wannan shekarar ya rike mukamin kwamishinan ‘yan sanda na jihar Ogun.

Share
Share
Language »