Freedom Radio Nigeria Kiwon Lafiya kwalejin fasaha ta kano: za mu kara kaimi wajen bunkasa harkokin ilimi

kwalejin fasaha ta kano: za mu kara kaimi wajen bunkasa harkokin ilimiKwalejin fasaha ta Kano ta bayyana aniyarta ta kara kaimi wajen bunkasa sha’anin koyo da koyarwa  ga dalibai.

Shugaban kwalejin Farfesa Mukhtar Atiku Kurawa ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a kwalejin.

Ya ce matakan da suka dauka sun hadar da tantance kwasa-kwasai da ake koyar dasu domin a yarda da su a duniya baki daya.

Farfesa Mukhtar Atiku Kurawa ya kuma kara da cewa, sun ga dacewar gyara harkokin gudanarwa a kwalejin musamman wajen  daukar dalibai.

Hukumar tantance kwasa-kwasan kwalejojin kimiyya ta NBTE a baya-bayan nan ta duba tare da sahale gudanar da kwasa-kwasai 51 bayan cika ka’idojin gabatar da su a sassan kwalejin ta fasaha dake nan Kano.