Freedom Radio Nigeria Kiwon Lafiya Gwamna Ganduje kara mayar da wasu kusoshinsa kan mukamansu

Gwamna Ganduje kara mayar da wasu kusoshinsa kan mukamansuGwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya sake nada Alhaji Usman Alhaji a matsayin sabon sakataren gwamnatin jihar ta Kano.

Haka zalika gwamna Ganduje ya kuma ce, Alhaji Shehu Mu’azu, ya ci gaba da kasancewa a mukamin akanta Janar na jihar Kano

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan Abba Anwar ya fitar.

Sanarwar ta ce, gwamna Ganduje ya gamsu matuka da yadda ya gudanar da ayyuka da mutanen biyu a wa’adin mulkin sa na farko, a don haka ya ga dacewar sake basu dama a wa’adin sa na biyu.