Hukumar EFCC ta musanta rahoton kama Rochas

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta  EFCC ta musanta rahotannin da ke cewa, ta kama tsohon gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha.

A cewar Hukumar ta EFCC babu kamshin gaskiya cikin labaran da ke yawo cewa ta kama Rochas Okorocha.

Tun farko dai kafofin yada labarai, sun yi ta yada cewa, hukumar EFCC ta kama Rochas Okorocha tare da matar sa.

Share
Share
Language »