Freedom Radio Nigeria Labarai Yemi Osinbajo ya bayyana Imam Abdullahi Abubakar, a matsayin gwarzo abun koyi

Yemi Osinbajo ya bayyana Imam Abdullahi Abubakar, a matsayin gwarzo abun koyiMataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana malamin addinin Islaman nan da ke jihar Filato wanda ya ceci rayukan wasu mabiya addinin kirista da ‘yan bindiga suka biyo, Imam Abdullahi Abubakar, a matsayin gwarzo kuma abun koyi.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai Magana da yawun shugaban kasa Laolu Akande.

Sanarwar ta ce Osinbajo ya bayyana hakan ne lokacin da ya karbi bakuncin Limamin wanda ya kai ziyara fadar shugaban kasa a jiya Alhamis.

A ranar 23 ga watan Yunin bara ne Imam Abdullahi Abubakar limamin masallacin kauyen Yelwan Gindin Akwati a yankin karamar Hukumar Barikin Ladi a jihar Filato ya boye mutanen a masallacin sa bayan da ‘yan bindiga suka biyo su.