Freedom Radio Nigeria Kasuwanci Majalisar dattawa ta amince a biya wasu kamfanoni kudaden tallafin mai

Majalisar dattawa ta amince a biya wasu kamfanoni kudaden tallafin maiMajalisar dattawa ta amince da a biya wasu kamfanoni 67 kudaden tallafin mai da ya kai naira biliyan 129.

Hakan ya biyo bayan amincewa da rahoton kwamitin kula da albarkatun man fetur wanda Sanata Kabiru Marafa ke jagoranta.

Wannan dai shi ya kawo jimillar naira biliyan 545 da miliyan 900 wanda majalisar dattawa ta amince da a biya dillalan na mai kudaden tallafin tun daga watan Yulin bara zuwa bana.

Haka zalika majalisar ta bukaci gwamnatin tarayya da ta biya dukkannin sauran kudaden tallafin mai domin kawo karshen shirin baki daya.