Freedom Radio Nigeria Labaran Jihar Kano An dakatar da hawan Sarki Majalisar masarautar Kano

An dakatar da hawan Sarki Majalisar masarautar KanoMajalisar masarautar Kano ta sanar da dakatar da Hawan Nassarawa da Hawan Dorayi da aka shirya za a gudanar a yau Alhamis da kuma gobe Juma’a.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren majalisar masarautar ta Kano Alhaji Abba Yusuf.

Sanarwar ta ce dakatar da Hawan na Nassarawa ya biyo bayan umarnin hakan da gwamnatin jihar Kano ta bayar wanda kuma ya zama wajibi ga masarautar ta Kano ta yi biyayya.

A cewar sanarwar bayanan sirri da suka samu sun tabbatar da cewa, akwai wasu batagari da ke neman amfani da Hawan Dorayi domin ta da hatsaniya wanda hakan ka iya janyowa jama’ar da basu ji ba basu gani ba su samu munanan raunuka.

Haka zalika sanarwar ta kuma bukaci limamai da malaman addinin musulunci da kuma al’ummar jihar Kano da su taho masallacin sarki domin gudanar da addu’oi ga marigayi Sarkin Kano Ado Bayero wanda ya rasu a ranar shida ga watan Yunin shekarar dubu biyu da goma sha hudu.

Sanarwar ta kuma ce akwai adduoin cika shekaru biyar da nadin sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi na biyu a gobe juma’a.