0 Comments

Mambobin jam’iyyar PDP a majalisar wakilai sun yi watsi da rade-radin da ke cewa uwar jam’iyyar ta umarce su da su kadawa wani dantakarar shugabancin majalisar ta wakilai kuri’ar su.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai Leo Ogor.

Sanarwar ta ruwaito cewa babu kanshin gaskiya cikin rade-radin adon haka mambobin majalisar su ka bukaci al’ummar kasar nan da su yi watsi da batun.

Mr Leo Ogor ta cikin sanarwar ya kuma ce jam’iyyar PDP bata hana ‘ya’yan jam’iyyar zabar ‘yan takarar shugabancin majalisar karkashin jam’iyyar APC ba.

 

Share
Share
Language »