Freedom Radio Nigeria Labaran Jihar Kano Sarkin Rano ya dakatar da wasu Hakimai

Sarkin Rano ya dakatar da wasu HakimaiMai Martaba Sarkin Rano Alhaji Tafida Ila Autan Bawo ya dakatar da Hakimin Tudun Wada Dr Bashir Muhammad da na Karamar hukumar Bebeji Alhaji Haruna Sunusi bisa bijirewa yi masa mubayi’a da suka yi.

Wannan na kunshe cikin wata wasika ta musamman da aka aikewa hakiman da ke dauke da sa hannun sakataren masarautar Ranon Muhammad Idris Rano.

Wasikar da aka aike ta ce an dauki matakin dakatar da su ne sakamakon kin bin umarnin da Sarkin ya ba su na su halarci masarautar Ranon domin gudanar da bukukuwan Sallah karama amma suka bijirewa umarnin.

sarkin ya kuma tunbuke su daga sarautun da suke rike dashi na Dan Galadima a Bebeji da kuma Sarautar dan Kadai a Tudun Wada.

Masarautar ta kuma zargesu da nuna rashin da’a na kan zuwa masarautar Kano wadda ba ta su ba suka kuma gudanar da hawan Sallah duk kuma da umarnin da sarkin ya basu.

Sakataren ya kuma ce tuni aka aike da kwafin takardar zuwa ma’aikatar kanan hukumomi na jihar Kano da kuma ofishin shugabannin kanan hukumomin su domin sanar da su halin da ake ciki.