0 Comments

Mai martaba sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi ll ya musanta zargin da Hukumar karbar korafi da yaki da cin hanci da rahsawa ta jihar Kano ke masa na barnatar da sama da naira biliyan uku mallakin masarautar Kano.

Wannan na kunshe cikin takardar tuhumar da sarkin ya amsawa gwamnatin jihar Kano, mai dauke da sa hannun mukaddashin sakataren majalisar masarautar Kano Malam Abba Yusuf.

A cewar sarkin lokacin da ya hau karagar mulkin Kano, ya samu naira biliyan daya da miliyan dari takwas da casa’in da uku, da dubu dari uku da talatin da takwas, da dari tara da ashirin da bakwai, da kuma kwabo talatin da takwas a lalitar masarautar.

Mai martaba sarkin Kano ta cikin takardar ya kuma bayyana cewa shi ba jami’in lura da sashen kudi bane, don haka bashi da alhakin yadda za’a sarrafa kudin masarautar Kano.

Idan za a iya tunawa dai a ranar Alhamis din da ta gabata ne gwamnatin jihar Kano ta aikewa Malam Muhammadu Sanusi na biyu takardar tuhumar, kan zargin da ake masa da barnatar da sama da naira biliyan uku mallakin masarautar, tun daga lokacin da ya hau mulki zuwa yanzu.

Share
Share
Language »