Hukumar shige da fice ta ja kunnen wasu jami’anta kan cin hanci

Kwanturola Janar na hukumar kula da shige da fice ta Najeriya Muhammad Babandede, ya shawarci manyan jami’an hukumar hamsin da uku wadanda aka yiwa karin girma da su guji cin hanci da rashawa, kuma su guji son zuciya yayin gudanar da ayyukansu.

Muhammad Babandede ya bayyana hakan ne yayin bikin karin girma ga jami’an wanda ya gudana a shalkwatar hukumar da ke Abuja.

A cewar kwanturola Janar na hukumar kula da shige da fice ta Najeriya, kwarewa da kuma jajircewar su a aiki shiyasa aka ga dacewar yi musu karin girma, a don haka ya hore su da su zage dantse wajen ganin sun kare mutuncin kasar nan.

Rahotanni sun ce mataimakan kwanturolan jihohi guda hamsin da uku ne aka yiwa karin girma zuwa mukamin kwanturola.

Share
Share
Language »