INEC ta ce zata daukaka karar hukunci baiwa Rochas Okoracha takardar shaida

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta ce zata daukaka karar hukuncin da babbar kotun tarrayya ta bada umarnin da a baiwa tsohon gwamnan jihar Imo wanda ya tsaya takarar sanata mai wakiltar mazabar Imo ta yamma a jihar Imo  shedai samun nasara a zaben da aka yi a ranar 23 ga watan Fabarairun da ya gabata.

 

Wannan na kunshe cikin sanarwar da shugaban sashin yada labarai da ilimantarwa kan zabe na hukumar ta INEC Mr, Festus Okoye ya sanya wa hannu a Abuja.

 

Sanarwar ta kuma ta mikawa dan takarar sanatan Rochas Okorocha shedar ne don yin biyaya ga umarnin kotun tarraya dake Abuja ta bashi, amma kuma nan gaba kadan ne zata daukaka kara kan uamrnin.

 

Haka zalika Festus Okoye ya ce kafin yanke wannan shawarar sai da hukumar ta INEC tayi la’akari da kundin bayanai 14 kan hukunce-hukunce  da suka danganci  umarnin janye shedar zabe  kafin da bayan zabukan da suka gabata.

Share
Share
Language »