WHO:zata waiwaye cutar dake alaka da tabin hankali

Hukumar lafiya duniya WHO ta ce a wannan shekara za ta dauki gabaran yaki da cututtuka da ke alaka da tabin hankali da jama’a da dama ke fama da shi a wasu kasashen duniya da dama ciki har da Najeriya.

Hakan na kunshe ne cikin wani rahoto da Hukumar ta wallafa a jiya Laraba wanda ta bayyana kasashen da za ta gudanar da ayyukan da suka hada da: Najeriya da Bangladesh da Iraki da Jordan da Lebanon da kuma Sudan ta kudu

Sauran sune: Syria da Ukraine da kuma zirin Gaza da ke Yankin Palastinawa.

A cikin rahoton Hukumar ya kuma bayyana cewa akwai mutane da dama da ke fama da lalurar tabin hankali a wadannan kasashen wadanda akasari yana faruwa ne sakamakon rikice-rikice da ke addabar kasashen.

 

Haka kuma rahoton ya ce duk yaro daya cikin biyar yana fama da lalurar tabin hankali cikin wadannan kasashen sakamakon damuwa da suke fama da shi.

Share
Share
Language »