Katsina:wani jirgin shalkwabta rundanar sojin kasar nan yayi hadari

Wani jirgin shalkwabta mallakin rundunar sojojin sama na kasar nan yayi hadari lokacin da ya ke kokarin sauka bayan dawowa daga samame da ya kai ga ‘yan bindiga a jihar Katsina.

Daraktan yada labarai na rundunar sojin sama na kasar nan Air Commodore Ibikunle Daramola ne ya bayyana haka ga manema labarai jiya a Abuja.

A cewar sa jirgion yayi hadari ne da misalin karfe uku da rabi a filin jirgin sama na katsina a jiya Laraba sai dai har ya zuwa yanzu ba akai ga gano musabbabin hatsarin ba.

Air Commodore Ibikunle Daramola ya kuma ce ba a samu hasarar rayuka ba sanadiyar hatsarin.

Haka kuma ya ce babban hafsan sojin sama na kasa Air marshall Sadique Abubakar ya bada umarnin gudanar bincike don gano musabbabin faruwar lamarin.

Share
Share