0 Comments

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari wasu yankunan karamar hukumar Kaura Namoda inda suka hallaka mutun guda tare sace wasu mutum bakwai.

Maharan sun durfafin grin ne da karfe 11:30 na daren Juma’ar da ta gabata a daidai lokacin da ruwan sama ke sauka kamar da bakin kwarya.

Shugaban karamar hukumar ta Kaura Namoda Lawal Isah ya tabbatar da hakan ga manema labarai a jiya lahadi yana mai cewa cikin wadanda aka yi garkuwa da su har da dagacin garin da matansa uku da kuma dansa mai shekaru 13 da haihuwa.

A ranar alhamis din da ta gabata ne dai wasu maharan suka farwa karamar hukumar Tsafe inda suka kashea mutum 18, har ma shugaban kas Muhammadu Buhari ya mik sakon ta’aziyyarsa ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu.

Share
Share
Language »