Freedom Radio Nigeria Labaran Jihar Kano Rundunar yan sandan Kano ta kubutar da Magajin Garin Daura Alhaji Musa Umar

Rundunar yan sandan Kano ta kubutar da Magajin Garin Daura Alhaji Musa UmarRundunar ‘yan sandan Kano ta tabbatar da ceto magajin garin Daura bayan musayar wuta da masu garkuwa da mutane a safiyar yau Talata, a Unguwar Gangar Ruwa da ke Gwazaye a karamar hukumar Kumbotso a nan Kano.

Tun daren jiya ne dai aka rinka jin karar harbe harbe a yankin inda a safiyar yau ‘yan sandan suka fito ta magajin garin Daurar daga wani gida bayan harbe mutun guda daga cikin wandan da ake zargin.

Wasu ganau sun shaidawa Freedom Rediyo yadda aka yi dauki-ba-dadin tsakanin ‘yan sandan da wadanda ake zargi da garkuwar