0 Comments

Rundunar tsaro ta civil defence ta yi holin wasu da ake zargi da satar mutane don garkuwa da su da kuma sauran muggan laifuka a birnin Lokoja na Jihar Kogi.

Kwamandan rundunar a jihar Kogi Olusola Philip Ayodele ya sanar da cewa sun samu nasarar cafke wadanda ake zargin bayan tattara bayan sirri.

Daga cikinsu akewai Usman Muhammad Sani da Abubakar Musa da suka sace wata mata mai suna Binta Haruna wadda take shayarwa a garin Jida Bassa da ke karamar hukumar Ajaokuta a Jihar Kogin, tare da sace kudi naira dubu hamsin da wayoyin hannu uku a gidan.

An kuma kama su a Jihar Niger, yayin da har yanzu a ke neman ragowar abokan burminsu, kuma an ceto matar, bayan sun bukaci a basu Naira miliyan biyu a matsayin kudin fansa.

Haka zalika sauran da aka yi holing na su an zarge su da sace-sace da kuma lalata abababen hawa a kamfanin Siminti na Dangote da ke Obajana.

Kwamandan ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba za a gurfanar da su gaban shari’a.

 

Share
Share
Language »