0 Comments

Wani fitaccen masanin tattalin arziki da muhalli a Jami’ar Bayero da ke nan Kano ya yi kira ga al’umma da su mai da hankali wajen tsaftacce muhallinsu domin magance matsalolin da ke janyo gurbacewar muhalli.

 

Farfesa Mustapha Muktar, ya bayyana hakan ne ta cikin shirin ‘’Barka da Hantsi” na nan freedom rediyo da ya mai da hankali kan dangantakar tsaftar muhalli da tattalin arziki.

 

Ya ce gurbacewar muhalli lamari ne da ke shafar tattalin arziki ta bangarori da dama a don haka zai fi kyautatuwa hukumomi su dauki gabarin dakile matsalar gurbacewar muhalli.

 

Farfesa Mustapha Mukhtar ya kuma ce, rashin bin ka’idojin muhalli musamman da masana’antu da kamfanonin hakar ma’adinai ke yi, yana daya daga cikin matsalolin da ke haifar da ambaliyar ruwa da zaizayar kasa da kuma yada cututtuka.

 

Masanin tattalin arziki da muhallin ya kuma yi kira ga gwamnatoci da su rika samar da wani tsari da zai yi tanadi ga hanyoyin tsaftace muhalli.

 

Share
Share
Language »