An sake nada Abba Kyari matsayin shugaban ma’akatan fadar gwamnati

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake nada Abba Kyari a matsayin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa.

Haka zalika Muhammadu Buhari ya kuma amincewa Boss Mustapha, ya ci gaba da kasancewa a matsayin sakataren gwamnatin tarayya.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu.

A cewar sanarwar, nadin nasu, ya fara aiki ne tun daga ranar ashirin da tara ga watan jiya na Mayu.

A shekarar dubu biyu da goma sha biyar ne dai shugaba Buhari ya nada Malam Abba Kyari a matsayin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, yayin da Boss Mustapha ya maye gurbin Babachir David Lawal a shekarar dubu biyu da goma sha bakwai

Share
Share
Language »