0 Comments

Idan Rayya zata amince zan iya aurarta a zahiri -Yawale

Jarumin wasan kwaikwayonnan da tauraruwarsa ta haska a film din nan na Kwana Casa’in Auwal Ishaq wanda aka fi sani da yawale, ya bayyana cewa babu soyayya a tsakaninsa da daya jarumar Film din wato rayya sai dai kawai akwai mutunta juna a tsakaninsu.

Yawale ya bayyana hakan yayin tattaunawarsa da Freedom Radio ya kuma kara da cewa ai duka yin Allah ne kuma bai san ko nan gaba ba zasu iya yin soyayya kuma shi idan har tana sonsa to tabbas zai iya aurenta.

Shin ko yaya kuke kallon wannan batu?

Share
Share
Language »