Hukumar Kwastam tayi karin girma ga jami’anta

Hukumar yaki da fasakwauri ta kasa kwastam ta yi karin girma ga wasu jami’nta guda dubu daya da dari tara da ashirin da hudu.

Mai magana da yawun hukumar Joseph Attah ne ya bayyana haka ga manema labarai ta cikin wata sanarwa da ya fitar jiya a Abuja.

Sanarwar ta ce, hamsin da daya daga ciki mataimakan sufeton kwastam ne wadanda aka yi musu karin girm zuwa sufeto haka kuma wasu masu mukaman na AIC arba’in da takwas an daga likkafar su zuwa IC.

A cikin sanarwar mai magana da yawun hukumar Joseph Attah ya ce karin girmar ya fara aiki ne nan take.

Haka zalika sanarwar ta ruwaito shugaban hukumar ta kwastam kanal Hamid Ali mai ritaya na yin kira ga wadanda aka yi wa karin girmar da su rubanya kokarin su wajen dakile ayyukan fasakwauri a kasar nan.

Share
Share
Language »