PDP ta bukaci a sauke hafsodhin tsaron Najeriya bisa gazawar su

Jam’iyyar PDP ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya sallami manyan hafsoshin tsaron kasar nan sakamakon gazawar su wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

A cewar jam’iyyar dabara ta kare ga manyan hafsoshin tsaron a don haka babu dalilin da za su c gaba da kasancewa a wannan mukami.

Mai Magana da yawun jam’iyyar Kola Ologbondiyan ne ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai, a Abuja.

Mista Kola Ologbondiyan ya ce abin kunya ne a ce tsawon lokacin manyan hafsoshin tsaron sun gaza wajen fitar da matsaya da zai kawo karshen zubar da jinin al’ummar kasar nan.

Share
Share
Language »