Gwamnatin jihar Bauchi ta bankado ma’aikatan bogi

Gwamna Bala Muhammad na jihar Bauchi ya ce binciken da aka gudanar a ma’ikatu da hukumomin gwamnati ya tabbatar da samu ma’akatan bogi  a ma’aikatun da hukumomin gwamnatin jihar ta Bauchi.

Da yake zantawa da manema labarai jin kadab bayan karbar bayanai daga dukkani ma’aikatun gwamnati da ke jihar, Gwamna Bala Muhammad ya ce mafiya yawa ma’aikatan jabun sun fito ne daga kana nan hukumomi.

A don hakan ne ya umarci shugaban ma’aikatan jihar da kuma hukumar sa da su dauki kwakwaran mataki wajen kawar da ma’aiakatan bogin cikin gaggawa su kuma magace faruwar hakan a nan gaba.

 

Gwamnan ya kuma nuna damuwar sa kan irin matsalar da bangaren lafiya da na ilimi ke fuskantar a fadin jihar baki daya.

Ya kuma yi alkawari nan ba da jimawa ba za a bada kwantiragi da dama domin gyara wasu daga cikin makarantun jihar da suka lalace, haka kuma za a debi ma’aikatan lafiya suma domin dai inganta bangarorin biyu.

 

Share
Share
Language »