Takai:Mutane 19 ne suka rasa rayukansu a wani hatsari da ya afku a kauyen Dinyar Madiga

Da misalin karfe biyar da rabi na yammacin jiya lahadi ne wasu motoci 2 kirar Golp da kuma motar safa suka hadu gaba-da gaba, kafin a daukesu daga kan hanya sai wasu motocin 2 suma suka hadu  kirar sharon mai lamba DRZ 525 XA da ta Kano line wadda hakan yayi sanadiyyar mutuwar mutane goma sha tara(19) 2 daga ciki Mata, sai yara kanakana 3, da Maza magidanta 14.

Sai wadanda suka jikata 11 a ciki akawi yara 4 maza 2 da mata 5, hatsarin dai ya farune sakamakon kaucewa ramukan dake kan Tatin kauyen Dinyar madiga da zarar  an wuce garin Takai.

Shugaban kungiyar direbobi (NURTW) ta kasa reshen karamar hukumar Takai Malam Datti Musa Shawu ya bukaci hukumar kula da hanyoyi ta Gwamnatin tarayya da hukumomin da abin shafa da su yi kokari wajen ganin an gyara wadannan gurare da ke haddasa hadaruruka sanadiyyar lalecewarsu

Malam Datijji Musa Shawu ya kara da cewa, daga watan daya na wannan shekara ta 2019 zuwa yanzu an sami hadarin mota sama  da goma sha daya, in da akayi asarar rayuka sama da 62.

Sai dai shugaban kungiyar Diribobin (NURTW) na Karamar Hukumar Takai ya yaba da namijin kokarin da Digacin garin Takai wajan hadakan masu hannu da ahuni dan samar da siminti da duwatsu dan gyara guraren da suke haddasa asarar rayuka a garin wato gaban maaikatar Ilimi da kuma Dinyar madiga, sai dai da zarar anyi gyaran bata dadewa yake lalacewa sabi da yawan manyan motocin da suke bin hayar.

Akan haka ne muka tuntubi hukumar kiyayyae hadura ta kasa reshen jihar Kano  shin ko tana masaniya kan wannan mumunan hadari.

Kwamadan hukumar kiyayye hadura ta jihar  Kano Zubairu Mato ya tabbatar da mutuwar mutane 19 yayin  mumunan hadarin motar da ya afko a kan hanayr Takai dake nan Kano, yayin mutum 7 suka jikata

Share
Share
Language »