An dage yanke hukunci a shari’ar takardun makarantar Shugaba Buhari

Kotun daukaka kara shiyyar Abuja ta jinkirta yanke hukunci game da shari’ar da ake na zargin shugaban kasa Muhammadu Buhari da rashin mallakar takardun makaranta.

 

Kotun mai kunshe da alkalai uku karkashin jagorancin mai shari’a Atinuke Akomolafe-Wilson, bayan sauraran lauyoyin bangarorin biyu, ta ce, za ta sanar da su ranar da za a yanke hukunci, idan komai ya kankama.

 

Yayin zaman kotun na jiya litinin, lauyan da ke wakiltar wadanda suka shigar da kara, Ukpai Ukairo, ya dage kan cewa, shugaba Buhari ba yi da takardar kammala makaranta da ya ba shi damar tsayawa takarar shugaban kasa.

 

A don haka ne lauyan wadanda suka shigar da karar ya kuma bukaci kotun daukaka karar, da ta yi watsi da hukuncin da wata kotu ta yi kan batun tun da fari.

 

A nasa bangaren lauyan shugaba Buhari Abdullahi Abubakar, ya ce, bai ma kamata kotun ta saurari karar ba, domin kuwa, tun farko ba a shigar da ita akan wa’adin da doka ta tanada ba.

 

Share
Share
Language »