Freedom Radio Nigeria Labarai An gargadi maniyyata guzurin ababan da aka hana a kasar Saudiya

An gargadi maniyyata guzurin ababan da aka hana a kasar Saudiya

 

Gwamnatin tarayya ta gargadi maniyyatan kasar nan da su guji yin guzurin duk wani abu da mahukuntan kasar saudiya suka haramta shigo da shi kasar su.

 

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun Hukumar kula da al’ummar kasar nan mazauna ketare Abdurrahman Balogun.

 

Sanarwar ta ruwaito shugabar Hukumar kula da al’ummar kasar nan mazauna ketare, Abike Dabiri Erewa na cewa, duk wanda aka kama da wani abu da mahukuntan kasar ta Saudiya suka haramta shigo da shi, to kuwa ba ko shakka hukuncin kisa zai hau kanshi.

 

Ta cikin sanarwar dai Abiki Dabiri Erewa ta bayyana safarar goro mai yawa da kuma magunguna masu kashe zafin ciwo, a matsayin wasu daga cikin abubuwan da aka haramta shigo da su kasar ta Saudiya, a don haka ta ce wajibi ne maniyyata su guji guzirun su.

 

A jiya Laraba ne dai aka fara jigilar maniyyatan Hajjin bana zuwa kasar Saudiya daga jihohin Katsina da Lagos, yayin da ake saran maniyyata sama da dubu sittin da biyar, ban da ‘yan jirgin yawo ne za su gudanar da aikin Hajjin bana daga kasar nan.