Hukumar dake karba korafe korafe ta kano zata hada kai da jagororin addinai

Hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta Jihar Kano ta lashi takobin hada kai da jagororin addinai don samar d wani dadalin wayar da kan al’umma wajen yakar cin hanci da rashawa a Kano.
Shugaban hukumar Barista Muhyi Magaji Rimin Gado ne ya bayyana hakan a jiya, yayin karbar bakuncin shugabannin kungiyar sasanta addinai da kuma yaki da cin hanci a ofishinsa.
Muhyi Magaji ya ce jagororin addini suna da gagrumar rawar takawa a cikin al’umma don dora su a kan turba ta gari tare da kakkabe rashawa da cin hanci, a don haka ne ya yi alkawarin cewa hukumar za ta ci gaba da hada kai da duk masu ruwa da tsaki wajen dakile cin hanci da rashawa.
Wata sanarwa da daraktan ayyuka na musamman na hukumar malam Usman Bello ya fitar, ta ce Barista Muhyi Magaji ya bukaci kungiyar ta samar da wani tsari tare da hadin gwiwar hukumar kan yadda za yaki cin hanci da rashawa a tsakanin al’umma.
Tun da fari jigo cikin kungiyar Bishop John Namaza Niyiring, cewa makasudin ziyarar shi ne don neman hadin kan hukumar tare da lalubo hanyoyin magance wannan matsala ta cin hanci, la’akari da tasirinta a cikin al’umma.

Share
Share
Language »