0 Comments

Hukumar dake kula da aikin hajjin ta kasa NAHCON Ta tabbatar da mutuwar ‘yan Najeriya 5 a kasa mai tsarki a yayin aikin hajjin bana

 

Shugaban ayarin likitoci a kasa mai tsariki Dr, Ibrahim Kana ne ya bayyana hakan cikin sanarwar da ya fitar a birnin Madina cewar hukumar aikin hajji ta kasa ta sami rahoton mutuwar alhazai 5 a Saudiya.

 

Dr, Ibrahim Kana ya ce wadanda suka rasun akwai mata 3 da maza 2, kuma mutum guda ne ya rasu a birnin Madina yayin da sauran 4 suka rasu a birnin Makkah

 

A cewar sanarwar mutanen sun rasa rayukan su a sakamakon cutattuka daban-daban da suka hada da cutar zuciya da ta huhu da dai sauran su.

 

Share
Share
Language »