0 Comments

Hukumomin kasar Saudiyya sun bijiro da wani sabon tsari na amfani da na’ura yayin jifan shaidan a garin Muna a ranar Arfa, da nufin tabbatar da kiyaye cunkoso a aikin hajjin bana.

Wakilin hukumar aikin hajji ta kasa NAHCON Tanko Aliyu ne ya shaidawa manema labarai hakan jiya lahadi a garin Muna yayin duba yadda sansanin ‘yan Najeriya ya ke.

Tanko Aliyu ya ce sabon tsarin zai taimakawa mahajjata wajen aiwatar da jifan bisa ka’ida inda za a rarraba su zuwa rukuni-rukuni, maimakon yin abinda ya kaucewa shari’a.

Ya kuma bukaci jami’an hukumar tare da takwarorinsu na Jihohi su rinka wayar da kan mahajjatan kan wannan tsari kasancewar an kirkiro shi ne don saukaka zirga-zirgar alhazai tare da kare lafiyarsu.

Share
Share
Language »