Freedom Radio Nigeria Labarai Rundunar yan sandan Kano ta yi holin mutane 116 da ake zargi da manyan laifuka

Rundunar yan sandan Kano ta yi holin mutane 116 da ake zargi da manyan laifuka

Rundunar yansandan jihar Kano ta yi holin mutane 116 wadanda ake zargin su da laifuka daban daban a fadin jihar Kano.

Kwamishinan ‘yansandan jihar Kano, CP Ahmad Iliyasu, shi ne ya yi wannan holin  a shalkwatar rundunar dake unguwar Bompai a jihar Kano.

Cikin wadanda aka yi holing nasu akwai matar nan wadda ta yi garkuwa da wata yarinya mai suna Aisha ‘yar shekara 9 wadda aka tsinci gawarta a unguwar Tukuntawa cikin wata rijiya a kwanakin baya.

Sai dai ko manema labarai suka so jin ta bakin matar da ake zargi da yin garkuwa da wata yarinya kuma suka kashe ta tare da jefa gawarta cikin Rijiya, sai ta fashe da kuka ta na cewa’’ ba za ta iya cewa komai ba.

Sauran masu laifin da aka yi holing su ga manema labaran akwai masu buga kudin bogi samfurin dalar Amurka wanda ya yi safarar su daga jihar Lagas ya ce siyo ta akan kudi Naira 500,000, da kuma ya canjar dasu ya sami Naira miliyan 150,000000.

Da yake jawabi, kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Ahmad Iliyasu, ya ce ’’rundunar su ta kai farmaki sun kuma sami nasarar dakile bata garin da suke kokarin shigowa jihar Kano, ya kuma yi rantsuwa da abin da zai kasha shi sai sun karkade aikin ta addanci a fadin jahar Kano a duk inda bata gari suke’’.