Freedom Radio Nigeria Kimiyya Kungiyar KASSOSA ta jaddada kudurin ta na kawo sauyi a sha’anin karatun kimiyya

Kungiyar KASSOSA ta jaddada kudurin ta na kawo sauyi a sha’anin karatun kimiyyaKungiyar tsoffin daliban kwalejin kimiyya ta Dawakin Kudu KASSOSA aji na 1987 ta jaddada kudurin ta na kawo sauyi a yanayin tafiyar da karatun kimiyya.

Shugaban kwalejin ilmi da share fagen shiga jami’a ta Kano da aka fi sani da (CAS) Dakta Sanusi Yakubu Ahmad ne ya bayyana hakan, yayin taron kungiyar da aka gudanar a dakin taro na kwalejin.

Dakta Sanusi Yakubu Ahmad yace muhimmancin shirya taron shine sada zumunci tare da taimakon juna da kuma kwalejin da ta zama jigon kai su ga matakin da suke.

Da yake jawabi, Daraktan shiyyar Africa na hukumar ma’aikata masu zirga-zirga Alhaji Muhammad Safiyanu ya sha alwashin tallafawa ‘ya’yan kungiyar da guraben ayyuka a wani mataki na tabbatar da ‘yan uwan taka a tsakanin su.

Wakilin mu Umar Idris Shuaibu ya ruwaito shugaban kungiyar KASSOSA aji na 1987 Dakta Dayyabu Alhaji Ibrahim yace kungiyar ta samu nasarori daban-dabam wajen tallafawa sha’anin koyo da koyarwa a kwalejin kimiyya ta Dawakin Kudu da suka hadar da ginin masallacin Juma’a.