Gwamnatin tarayya ta baiwa tsofafin ma’aikatan kamfanin jirgin sama hakokinsu

Gwamnatin tarayya  ta baiwa tsofafin ma’aikatan kamfanin jirgin saman na Nigeria Airways tabbacin biyan su hakokin su bayan kammala bincike.

Babban sakatare  a ma’aikatar kudi ta kasa Mohammed Dikwa ne ya bayyana hakan a yayin da ya kai ziyara cibiyoyin tantance tsofafin ma’aikatan dake Lagos da nan Kano.

Wannan na kunshe cikin sanarwar da mataimakin jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar wanda ya fitar a Abuja.

Mohammed Dikwa da yake wakilatar mataimakin babban daraktan ma’aikatar Mr Izerebu John ya ce kwamitin bincike na fadar shugaban kasa dake cigaba da gudanar da bincike ya kaddamar da fara tantance  tsofafin ma’aikatan na mako guda.

Ya kara da cewar don tabbatar da tsage gaskita ne ya sanya aka fara  tantace tsofafin ma’aikatan don biya su hakokin su.

 

Share
Share
Language »