Ansace gangar mai miliyan 22 a jihar Edo

Gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki, ya ce, cikin watanni shidan farko na wannan shekara, barayin ‘Mai’ sun sace gangar mai miliyan ashirin da biyu.

Gwamna Obaseki ya kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki da su tabbata sun yi duk me yiwuwa wajen ganin an dakile matsalar satar danyen mai a kasar nan.

Godwin Obaseki wanda shine shugaban kwamitin wucin gadi na majalisar kula da tattalin arziki ta kasa kan dakile matsalar satar danyen mai, ya ce, lamarin ya yi munin gaske da ya kamata kasar nan ta dau mataki don shawo kan matsalar.

Acewar sa, matukar ba a dauki matakin dakile lamarin ba, to kuwa ba ko shakka, kasar nan za ta yi asara fiye da wanda aka gani a baya, a nan gaba. Gwamnan na jihar Edo yana wannan jawabi ne wajen taron masu ruwa da tsaki da kamfanin mai na kasa (NNPC) ya shirya, a Abuja

Share
Share
Language »