0 Comments

Gwamnatin tarayya ta ce a gobe Talata za ta ci gaba da aikin dawo da al’ummar kasar nan mazauna kasar Afurka ta kudu wadanda kashe-kashen kin jinin baki da ke gudana a kasar ya tursasu tserewa.

A ranar larabar da ta gabata ne dai, wani jirgin kamfanin ‘Peace Air’ ya kawo kason farko wadanda suka kai dari da tamanin da bakwai.

Rahotanni sun ce, ya zuwa yanzu, ana saran a gobe Talata za a dawo da mutane dari uku da goma sha tara.

Ko a ranar Larabar da ta gabata, an samu jinkiri wajen jigilar mutanen sakamakon dagewa da hukumomin kasar ta Afurka ta kudu su ka yi na cewa, wasu daga cikin ‘yan Najeriyar ba su da cikakkun takardun gudanar da tafiye-tafiye.

Akalla dai ‘yan Najeriya mazauna kasar Afurka ta kudu dari shida da arba’in ne su ka yi rajista da ofishin jakadancin kasar nan da ke biranen Pretoria da Johannesburg domin dawowa gida. Wannan na zuwa ne a lokaci guda da shugaban kasar ta Afurka ta kudu Cyril Ramaphosa ya turo da wakilai zuwa wasu kasashen Afurka, ciki har da kasar nan don neman hadin kansu game da matsalar da ta faru a kasar

Share
Share
Language »