0 Comments

Rundunar ‘yan sandan birnin tarayya Abuja ta tabbatar da sacewa tare da yin garkuwa da wata mata mai shekaru ashirin da hudu mai suna Aisha Umar Ardo.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan na birnin tarayya Abuja, DSP Anjuguri Manza.

A cewar sanarwar, an sace matashiiyar ce, a daren shekaran jiya  Asabar da misalin karfe bakwai da mintuna arba’in da biyar jim kadan bayan fitowarta daga wani babban kantin sai da kayayyaki da ke unguwar Asokoro. Sai dai wata majiya da ke kusanci da iyalan matashiyar sun shaidawa manema labarai da safiyar nan cewa, an sako yarinyar bayan da iyayenta su ka biya kudin fansa dala dubu goma sha biyar

Share
Share
Language »