0 Comments

Rundunar sojin kasar nan ta dakile wani hari da mayakan Boko Haram su ka kai a Jami’ar Maiduguri a daren jiya Lahadi.

Wata majiya ta shaidawa manema labarai cewa, an yi ta jin karar bindiga a wani yanki da ke kusa da dakunan kwanan dalibai mata.

A cewar majiyar sojoji da wasu da ake zaton ‘yan Boko-haram ne sun kai kusan awa guda suna batakashi da juna.

Haka zalika wani soja da ya bukaci a sakaya sunan sa, ya shaidawa manema labarai cewa, sun yi kazamin barna ga sojojin. Haka zalika wasu dalibai Khadija Muhammed da Victoria ta ce lokacin da lamarin ya faru sun tsere domin tsira da rayukansu

Share
Share
Language »