0 Comments

Jakadiyar Najeriya a kasar Burkina Faso, Ambasada Ramatu Ahmed, ta ce, akalla ‘yan matan kasar nan sama da dubu goma ne aka tursasu yin karuwanci a kasar ta Burkina Faso.

Hajiya Ramatu Ahmed ta bayyana hakan ne yayin zantawa da manema labarai a birnin Ouagadougou da ke kasar Burkina Faso.

Ta ce abin takaicin shine mafi yawa na ‘yan matan da ake bautar da su ta hanyar tursasu shiga harkar karuwanci kananan yara ne matuka.

Jakadar Najeriyar wadda ta fara aiki a kasar ta Burkina Faso tun a shekarar dubu biyu da goma sha bakwai ta kuma ce da dama daga cikin ‘yan matan suna sansanonin da ake hakar ma’adinai ne sai dai ta ce a baya-bayan nan gwamnati ta samu nasarar dawo da guda dari biyu daga cikin su.

Ta kara da cewa ofishin jakadancin kasar nan da ke Burkina Faso ya yi matukar damuwa kan halin da wadannan ‘yan mata su ke ciki wadanda mafi yawansu an yi musu romon baka ne da cewa za a kaisu nahiyar Turai.

Share
Share
Language »