0 Comments

Hukumar kiyaye abkuwar hadurra ta kasa (FRSC), ta ce, ya zuwa yanzu, adadin wadanda suka rasa rayukansu, sakamakon wani hatsarin mota da ya abku a Akwanga da ke jihar Nassarawa sun kai goma sha takwas.

Shugaban hukumar ta FRSC reshen jihar Nassarawa Isma’ila Kugu ne ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai a garin Lafiya babban birnin jihar.

Ya ce hatsarin da ya abku tun a ranar lahadi da ta gabata ya faru ne tsakanin wata motar Safa mallakin gwamnatin jihar Benue da kuma wata mota ta daban.

A cewar Isma’ila Kugu, lokacin da lamarin ya faru, mutane goma sha uku sun mutu ne nan take, yayin da goma sha daya suka jikkata wadanda kuma aka kwashesu zuwa asibitocin da ke garuruwan Nassarawa Eggon da kuma Lafiya babban birnin jihar.

Ya kuma ce bayan da suka sake ziyartar asibitin a jiya domin ganin halinda wadanda suka jikkata su ke ciki, sun kuma tarar cewa biyar daga cikin goma sha daya da suka jikkata sun mutu.

Share
Share
Language »