0 Comments

 ‘Yan sanda a kasar Indonesiya, sun ce, masu zanga-zanga a lardin Papua da ke kasar, sun lalata gine-gine da safiyar yau litinin.

Zanga-zangar da aka fara tun a watan Agustan da ya gabata, ta yi sanadiyar mutuwar mutane biyar a lardunan Papua da kuma Papua ta yamma.

Rahotanni sun ce zanga-zangar ta samo asali ne biyo bayan zargin nuna wariya da jami’an tsaro ke yi ga dalibai ‘yan asalin lardin Papua a tsibirin Java.

Kafofin yada labaran kasar sun ruwaito cewa, masu zanga-zangar sun cinna wuta ga ofishin hukumomi da ke Wamena.

Mai Magana da yawun rundunar ‘yan sandan kasar ta Indonesiya, Dedi Prasetyo, ya ce, tuni aka tura da jami’an tsaro domin dawo da doka da oda.

Share
Share
Language »