Gwamnati tarayya ta ware kudade don samar da kayyaki ginadar da kasuwanci a garin Fanisau

AD INJECTION TEST ADVERT 728x90
Ad Injection
www.advancedhtml.co.uk

Gwamnatin tarayya ta ware kudade don samar da kayayyakin da ake bukata a shiyyar gudanar da harkokin kasuwanci ta kano  dake garin Fanisau a cikin kasafin kudin bana.

Ministan tsare –tsare da kasafi Mista Udo Udoma shi ne ya bayyana hakan a yayin da yake bude taro karo na biyu na tattalin arziki da zuba jari a kano.

Udo Udoma ya ce haka kuma a wannan shekara gwamnatin tarayya ta samar da kudaden tallafi ga masu fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje, wadanda za su amfana da rangwamen biyan haraji.

A yayin da yake jaddada matsayin kano a fagen tattalin arziki da kasuwanci, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta tallafa wa kudirin gwamnatin jihar kano na dawo da dalar gyada don jihar da dawo da martabarta a fagen kasuwanci.

A nasa jawabin, mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar na uku ya jaddada kudirin sarakuna na tallafa wa masu rike da mukaman siyasa dake gudanar da ayyukan raya kasa don amfani al’iumma.

Taken taron dai shi ne ‘yi wa tattalin arzikin jihar kano garanbawul, ta yadda kalubale iri –iri zai zamo samun damarmaki iri daban daban.

 

 

TEST ADVERT 336x280 - reviewmylife

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO