0 Comments

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce ta samar da ‘yansanda sama da  dubu takwas tare da jiragen helikwafta guda biyu da za su yi aikin bayar da kariya ga jama’ar jihar Kano yayin ziyarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kawo jihar gobe Laraba.

Kwamishinan ‘yansandan jihar Kano, Rabi’u Yusuf ne ya bayyana haka yau bayan kammala shirin ‘Barka Da Hantsi’ na nan Freedom Rediyo.

Kwamishinan ya kuma ce rundunar ‘yan sandan ta gudanar da tarurruka daban-dabam da sauran jami’an tsaro da ke jihar Kano tare da umartar da kada su musguna wa kowa yayin ziyarar.

Shi kuwa kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Malam Muhammad Garba jan hankalin jama’a ya yi da su bayar da hadin kai lokacin ziyarar da shugaban kasar zai kawo Kano, inda ya ce ana sa ran shugaban kasar zai bude wasu ayyukan ci gaban jama’a tare da duba wasu ayyukan.

Bakin biyu dai sun yi fatan samun hadin kan jama’ar jihar Kano da kuma addu’ar samun nasarar ziyarar ta shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Share
Share
Language »